LabLynx Wiki

Gyara hanyoyin mahaɗar
Musulunci
Founded 631
Mai kafa gindi Muhammad
Classification
Sunan asali الإسلام
Practiced by Musulmi da ummah (en) Fassara
Branches Rukunnan Musulunci
Shahada
Sallah
Zakka
Azumi A Lokacin Ramadan
Aikin Hajji
Wata yarinya a Karanta Alqur'ani Mai girma
dakin Allah (S WA)
gurin ibadan musulmai

Addinin Musulunci (Islama;[1] Larabci: ٱلْإِسْلَام‎, romanized: al-Islām,) shine shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S A W) bawan Allah ne kuma manzon Sa. Addinin yana da alaka da Annabi Ibrahim kuma ya kunshi hukunce hukunce daga Alkur'ani da kuma koyarwar Manzon tsira wanda shi ne ya zo da littafin sannan akwai akalla mabiya addinin musulunci mutum biliyan 1.9 kuma shine addini na biyu dangane da yawan mabiya bayan addinin Kirista.[2]

Annabi [Muhammad] (S A W), tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi,[3] shine manzo wanda Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki daya kuma na karshen/cikamakin annabawa a duniya domin ya sake jaddada addinin Allah, a yi imani da Allah wanda ya halicci kowa da komai. Addinin musulunci na da mabiya a duk fadin duniya kuma mafiya yawa su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya da yankin [Afirka|Afrika] ta Arewa wadanda mafi yawansu [Larabawa] ne masu bin addinin musulunci, sai dai akwai dunbin mabiya addinin musulunci a ko'ina a fadin duniya.[4] Ma'anar Addinin Musulunci shine yarda da mika wuya ga Kadaita Allah Madaukakin Sarki, wato shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma annabi [Muhammad] s.a.w [Manzo].

Musulmai sunyi imani cewa addinin Musulunci shine cikakken addini kuma addini na gasiya wanda aka turo Annabawa da manzanni da yawa a baya, wanda suka hada da kakanmu Annabi Adamu, Annabi Nuhu, Annabi Ibrahim, Annabi Musa da kuma Annabi Isah. Har wayau, Musulmai sunyi imani cewa Alkur'ani maganar Allah ne, kuma sakon Ubangiji ne na karshe wanda babu tawaya a cikin shi. Tare da AlKur'ani, Musulmai sunyi imani da sauran littattafan da aka turo kamar Attawra, Zabura da Injila. Kuma Annabi Muhammad (SAW) shine cikamakon Annabawan Musulunci, kuma ta shi ne addinin Musulunci ya cika. Koyarwarsa da umurninsa ana kiran su da Sunnah wanda aka rubuta a littattafai da ake kira Hadisi, wanda ke koyar da tsarin mulki da rayuwa.

Manazarta

  1. "English pronunciation of Islam". Cambridge Dictionary. Archived from the original on 22 January 2021. Retrieved 19 Dec 2023.
  2. "Pew-Templeton Global Religious Futures Project - Research and data from Pew Research Center". 21 December 2022. Archived from the original on 5 February 2023. Retrieved 27 November 2023.
  3. https://dictionary.cambridge.org/pronunciation/english/islam
  4. https://www.britannica.com/topic/Islam