Type a search term to find related articles by LIMS subject matter experts gathered from the most trusted and dynamic collaboration tools in the laboratory informatics industry.
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
water area (en) ![]() ![]() ![]() |
Produced sound (en) ![]() |
Q110068397 ![]() |
Nada jerin |
list of seas (en) ![]() |
Teku wani ginshikin bigire ne, wanda Allahu (SWT) ya gina, sashi ne wanda ya kunshi duniyar ruwa da yake gudana a doron ƙasa. Teku ne ma'ajiyar duk wani ruwa da yake gangarowa ta'kowanne bangare a faɗin duniya.
Kodayake teku ta rabu gida-gida wato kananan teku zuwa kuma manya , kamar irin su tekun atlantika wato "Atlantic Ocean" da kuma tekun maliya wato "Red sea" kasancewar teku nan ne matattarar duk wani ruwa, ta kunshi manya-manyan halittun ruwa kama tun daga kifi, kada, zuwa wasu halittu na daban wadanda ba mu san su ba. Bayan haka dandanon ruwan teku ya kasance mai gishiri-gishiri ne ba kamar yadda ruwan rijiya yake ba.
Masana ilimin kimiyya sun tabbatar da cewa inda ruwa ya mamaye ya fi inda kasa ta mamaye. A bisa kididdiga kuma inda ruwa ya mamaye ya kai kashi saba'in da biyar cikin dari (75%), amma inda kasa ta mamaye kwata-kwata kashi ashirin da biyar ne cikin dari (25%).
Teku ya kasance babban kundi inda Dan'adam ke amfani da shi a rayuwar sa, ana amfani da teku domin tafiye-tafiye a cikin jiragen ruwa daga kasa zuwa kasa ko daga wata nahiya zuwa wata nahiyar.
Sannan kuma akwai hallitun ruwa da ake samu daban-daban kamar su kifi da dorinar ruwa da dai sauransu. Haka zalika, man fetur shi ma duk daga teku ake samo shi da kuma irinsu gwala-gwalai da dai abubuwa masu dimbin amfani ga Yan-adam.